Headlines
Loading...
Qalu innalillahi yanzu yanzu faifan bidiyon murja ya fita mutane Qalu innalillahi yanzu yanzu faifan bidiyon murja ya fita mutane

Qalu innalillahi yanzu yanzu faifan bidiyon murja ya fita mutane Qalu innalillahi yanzu yanzu faifan bidiyon murja ya fita mutane

Qalu innalillahi yanzu yanzu faifan bidiyon murja ya fita mutane

Ficacciyar Jarumar shirin nan mai dogon zango Izzar so wanda

Tashar Bakori Tv dake kan manhajar Youtube take kawo muku a duk

sati wato Aisha Najamu wacce a cikin shirin ake kiran ra da Hajiya

Nafisa.

Ta bayyana a cikin wata bidiyo data wallafa a dandalin TikTok inda

take kuka tana zubda hawaye wanda hakan abin a tausaya mata ne,

inda take fadin cewa a ina aka taba ganin tana iskanci ko zina da

za’a ce suna iskanci.

Hakan ya biyo baya ne lokacin da wani matashi ya yi musu kudin

goro a dandalin TikTok, dama haka rayuwa take laifin da wani ya

aikata sai kaga ya shafi wani amma abin da Aisha Najamu tayi yana

nuna cewa ta fito ne domin ta wanke kan ta kan abin da ake zargin

su da aikatawa.

A cikin bidiyon da zaku kalla zaku ga yadda Aisha Najamu take kuma

tana fadin cewa, su sana’a suke amma ba ana kiran su da karuwai

ba.

NAMIJI ‘DAN GOYO NE GA WADDA TA IYA!!!

Yake ‘yar’uwa musulma kisani cewa mijinki wani mutum ne mai

daraja da kima da mutunci da ya kamata kisan girman shi,ki kuma

bashi girman shi.wajibine kiyiwa mijinki biyayya ki rinka tausaya

masa,ki rinka kula dashi ki rinka tattalinsa kamar kwai,ko ince kamar

kudi.

Ance za’a iya cin nasaran mutum ta hanyar kyautatawa,kamar yadda

ba’a iya cin nasaran mutum ta hanyar fitina.Da hali mai kyau, da

kalma mai kyau,da siffa mai kyau,da abinci mai dadi,da kallo mai

kyau,da tsafta na zuciya dana jiki dana kaya dana wuri,Hira mai dadi

da sauran abubuwan kyautatawa,kamar yadda baza kici nasara ta

hanyar komai ba.

Don haka ‘yar’uwa kisani cewa mijinki sitiyarin rayuwar sa gaba daya

yana hannun ki,Don haka ke ya kamata kisan yadda zaki tarairaye

shi,yadda zaki juyashi, yadda zaki lailaye shi ki kwantar masa da

hankali.Ya zama cewa rayuwar shi ta gyaru ta hanyar ki, hankalinsa

ya kwanta ta hanyar ki,rayuwarsa tayi kyau ta hanyar ki,shawarwarin

ki da halayen ki masu kyau sun daidaita shi akan sahu madaidaici.

Wasu matan zaka gansu kazamai, gashi basu iya girki ba,in tayi miya

kamar ruwan wanke kai,kuma mijin yana bata kudin cefanen amma

saita cinye kudin taki yi ba.bata iya tarban miji ba,bata iya lallaba miji

ba,bata san kalmomin soyayyar da yakamata ta rinka fadawa mijinta

ba,ya dawo wurin aiki ya gaji ba abincin kirki ba hirar kirki dole kuwa

ya kai dare a waje,saboda inya dawo gidan ba dadi,ko kuma kiyita

zunbura fuska kina cin magani kina fushi,wallahi mata mu muke

sanya maza su canza mana,domin inyaga takunki bana MACE

TAGARI bace shima sai ya juye,ayita tafka rigima,gida ya zama

kaman filin kaci uwaka.don haka QALUBALE GARE KU MATA.

Shiyasa sai kaga mata suna layin gidan bokaye suce sun kasa gane

kan mijin,ya za’ayi kuwa ki gane kanshi,bayan kinki gyara kanki, idan

har zaki yi waican abubuwan dana ambata a baya,to zaki sami

soyayyar mijinki,zai soki zai kuma so ‘ya’yanki,Don haka mata ku

gyara halayen ku,ku gyara zamanta kewarku da mazajen ku, kuma

mazan kuji tsoron Allah ku gyara,ta yadda za’a sami gyara ta ko’ina.

Allah ya bawa masu iyali zaman lafiya,Allah ya basu ‘ya’ya

mahaddatan, Al’qurani mai girma, Masu Taqwa,masu gaskiya,masu

Amana,masu mutunci,wainda zasu kafa mana gwamnatin musulunci

masu kuma yi adalici.Mu da ba muyi auren ba Allah ka bamu mazaje

nagari,suma mazan Allah ka basu mata nagari Salihai. Wadda zamu

yi zaman aure na gaskiya da Amana

0 Comments: