Headlines
Loading...
Kotu ta sake tura Murja Kunya da Real Idris Mai Wushirya, Aminu BBC da Sadiq Mai Waƙar A daidai ta nan zuwa gidan yari

Kotu ta sake tura Murja Kunya da Real Idris Mai Wushirya, Aminu BBC da Sadiq Mai Waƙar A daidai ta nan zuwa gidan yari

A karo na biyu kotu ta sake aike wa da fitacciyar mai amfani da dandalin TikTok ɗin nan wato Murja Ibrahim Kunya da ƙarin wasu mutune uku zuwa gidan yari.

Mutanen sun haɗa da Babban abokin Murjan wato Ashir Idris da aka fi sani da Mai Wushirya, sai kuma Aminu BBC, da Sadiq Shehu Shariff wanda ya yi waƙar nan mai taken “A daidai ta nan”.


Zauren Malaman Kano ne ya yi ƙarar matasan bisa zargin su da wallafa bidiyoyin baɗala a dandalin TikTok, inda hakan yaci karo da dokar addinin musulunci da kuma kauce wa al’adar Malam Bahaushe.

Ana dai tuhumar Murja Ibrahim Kunya da Real Ashir Idris ne da yin bidiyon batsa a TikTok, inda ya amsa laifinsa yayin da ita kuma ta musanta hakan, duk da kasancewarakwai tarin hujjoji da ake dasu akanta.

Sannan ana kuma tuhumar Aminu BBC da yin wasu bidiyon batsa a dandalin TikTok inda ya musanta tuhumar da akeyi masa, domin yana ganin wannan ba wani abu ne da za’a ce ya kauce hanya.

Sai kuma Sadiq Shehu Shariff mai waƙar “A daidai ta nan” wanda aka zarga da yin waƙar batsa zargin da shima ya musanta, inda yace wannan sam babu dangantakar abinda yake domin nishadantar da mabiyansa da batsa.

A nan ne lauyoyinsu suka nemi a basu belinsu, sai dai lauyan Gwamnati ya yi suka, inda ya nemi a basu mako guda domin su yi martani.


Kotun ta tura su zuwa gidan yari har zuwa 23 ga wannan watan Fabrairun da muke ciki domin cigaba da sauraron karar da kuma tuhumar da ake yiwa wadannan mutanen
Dangane da tuhumar da aka soma yiwa Murja a zaman da ya gabata kuwa, Murja ta rubuto takardar cewa ta tuba, inda Kotun ta ce za ta yi nazari a zama na gaba.

Mutane da dama sun tofa albarkacin bakin su akan wannan shari’a da kuma hukuncin da kotu ya kamata ta yanke musu domin hakan ya zama izina a garesu da dukkan masu hali irin nasu.

Anan saidai mu ce Allah ya gyara mana al’umma

0 Comments: