Headlines
Loading...
Mun nemi alfarma za’a saki Murja Ibrashim yau ko gobe, cewar Teema Makamashi

Mun nemi alfarma za’a saki Murja Ibrashim yau ko gobe, cewar Teema Makamashi

A yau din nan mun samu wani labari akan fitacciyar yar tiktok murja Ibrahim kunya wanda anka kai gidan gyran hali akan irin bidiyon da tayi akan irin rashin nuna kunya da zage zage kamar yadda ake zarginta shine ake tunanin za’a sake ta kamar yadda shafin Hausaloaded suka ruwaito.

Jaruma masana’antar shirya finafinan Hausa ta Kannywood Teema Makamashi tace, ta nemi alfarma a wajen wandanda take da sanayya dasu akan batun jarumar barkwanci ta shafin Tiktok “Murja Ibrahim Kunya” wacce ke gidan gyaran hali a yanzu.

Teema Makamashi ta bayyana haka cikin bidiyon da tayi a shafin ta na Tiktok inda tace, a gobe za’a saki Murja Ibrashim sai dai idan an samu tsaiko ne zata kai zuwa jibi.

Sai dai kuma Teeman Makamashi ta jaddada cewa, tabbas Murja Ibrashim tayi kuskure bisa abubuwan da take aikatawa a shafukan yanar gizo, amma dai alfarma ce suka nema akan a sake ta.

Ana zargin Murja ne da yada kalaman batsa, zage-zage da kuma rashin tarbiyya, musamman a shafinta na Tiktok, wanda zai kawo cikas ga tarbiyyar addinin musulunci.

Source of Hausaloaded

0 Comments: