Headlines
Loading...
Tofa Bidiyan Wani Mai Sayar Da Ragen Da Ya Wayne Yake Amfani Da POS Wajen Karbar Kudin Customer

Tofa Bidiyan Wani Mai Sayar Da Ragen Da Ya Wayne Yake Amfani Da POS Wajen Karbar Kudin Customer

Najeriya – Babban Bankin Najeriya (CBN) ya nunawa yan Najeriya yadda mai tallan rake ya bi ka’ida da sabuwar dokar takaita rike kudi ta Najerilya.

A wani bidiyon da bankin ya yada a Twitter an ga wani mutumin da ke tallan rake yana rike da na’urar POS yana tura baron tallan rakensa.

Kwastomin da ke siyan raken sun zagaye suna yi masa tambayoyi, wani kuma ya siya rake yana saka lambobin ‘PIN’ dinsa don biyan kudi a POS.


Mutane da yawa ne suka yi layi domin siyan raken nasa, inda shi kuwa cikin kwarin gwiwa yake kasuwancinsa ba tare da nuna damuwa ba.


Yan Najeriya da yawa sun yi Allah-wadai da yadda CBN Ke ba yan Najeriya wahala ta hanyar hana su rike kudade da yawa a cikin al’umma fiye da kima.

Wasu mutane da yawa kuwa sun yi martani tare da yada wasu bidiyoyin da aka fitar na yadda mutane su kokuwa da shan wahalar layi a bankunan kasuwanci a kasar.

Kalli bidiyon:



0 Comments: